Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jam’iyyar adawa ta PDP ta shiga zullumi da rashin tabbas sakamakon irin nasarorin da APC ke samu.
Da yake jawabi a taron kolin APC da aka gudanar a fadar shugaban kasa, Ganduje ya ce APC za ta lashe zaben da ke tafe a babban birnin tarayya (FCT) saboda kwarewar siyasa da karfinta.
Ya ce rikice-rikice da sauya sheka da ke damun PDP ya sanya mambobinta da dama ke komawa APC.
Ganduje ya kara da cewa APC na da gwamnonin jihohi 22 daga cikin 36, kuma wani gwamna na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar.
Ya ce nasarorin APC a zabukan da suka biyo bayan na 2023 na nuna hasashen nasararta a 2027.



