Kungiyar magoya bayan jam’iyyar APC na yankin Arewa ta tsakiyar Nijeriya ta ba shugaban jam’iyyar APC na jihar Plateau Rufus Bature wa’adin kwanaki 7 ya kafa kwamitin sulhunta ‘ya’yan jam’iyyar.
Kazalika, kungiyar ta kuma nemi bangaren Rufus da ya ba da dama ga sauran ‘yan wata jam’iyyar su shigo cikin APC a jihar don ciyar da jam’iyyar gaba.
Wannan wa’adi dai ya biyo bayan wani matakin kungiyar da dauko wani kyamfe na Green Cap Movement da ke nuna alamar yadda Gwamnan jihar na PDP Calep Mufwang yake saka hula.
Wannan kungiya dai ta dade tana kira ga Gwamnan jihar Calep Mutfwang da ya bar jam’iyyarsa ta PDP ya koma APC.
Shugaban kungiyar Saleh Abdullahi Zazzaga ya ce sun dauki wannan matakin ne domin kara jaddada kalamansu na mara baya ga tazarcen Shugaba Tinubu a zaben 2027.
Sai dai, a cikin wata sanarwa daga bangaren Rufus Bature, APC ta yi Allah-wadai da wannan shela ta Green Cap Movement da wannan kungiya ta dauko.
Sai dai, kungiyar North Central APC Forum ta zargi tsagin APC ta Rufus da yi wa wasu tsirarun mutane aiki ba don cigaban al’umma ba.