DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotu ta ba EFCC damar binciken wasu malaman Kano kan badakalar fili

-

Kotun tarayya ta yanke hukunci cewa hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa na da ikon bincikar zargin badakalar fili na Naira biliyan 3.5 da ya hada da wasu malaman addini a jihar Kano.

Jaridar PREMIUM TIMES ta rawaito a watan Afrilu yadda wadannan malamai suka shigar da kara a kotu a Kano don hana hukumar EFCC kama su ko kuma yi musu tambayoyi kan batun.

Google search engine

Wasu mambobin kungiyar Incorporated Trustees of Musabaqah Association ne suka rubuta korafi zuwa ga hukumar EFCC, suna zargin wasu daga cikin mambobin kungiyar da sayar da fili da gwamnatin jihar ta bayar domin gina cibiyar Musabaqar Karatun Alkur’ani ta kasa ba bisa ka’ida ba.

Masu korafin sun ce filin da ke cikin unguwa mai daraja a Kano, an sayar da shi cikin zamba ga kamfanin Nata’ala Properties and Investment Company Limited wanda Tijjani Sule-Garo ke jagoranta.

Sun bukaci EFCC ta gudanar da cikakken bincike kan yadda aka sayar da filin tare da dakatar da ginawa ko duk wani yunkurin tayar da bango a filin har sai an kammala binciken.

Haka kuma, masu korafin sun bukaci EFCC ta gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a sayarwar, tare da dawo da filin domin a yi amfani da shi yadda aka tsara tun farko.

Wadanda ake zargi sun shigar da kara kotu bayan EFCC ta gayyace su domin amsa tambayoyi kan korafin da aka shigar kansu.

Jaridar ta rawaito cewa msu shigar da korafin sun ce an sayar da filin mai fadin kusan hekta biyu da ke babban titin Ahmadu Bello, Nasarawa GRA a Kano, wanda darajarsa ta kai Naira biliyan 3.5, cikin kudin da bai kai Naira miliyan 400 ba.

Sun bayyana sunayen wadanda ake zargi da hannu a badakalar da suka hada da:
Ibrahim Shehu-Maihula, Gwani Yahuza-Danzarga, Aliyu Harazimi, Tijjani Bala-Kalarawi, Sa’idu Muhammad-Koki, Ado Shehu-Maibargo, Abdu Muhammad-Dutse, Abubakar Aliyu-Darma, Ahmad Tijjani-Yusuf, Tijjani Mailafiya-Sanka, Sabiu Bako, da Muhammad Tukur-Gadanya.

Rahotanni sun ce Wase ya ware wannan fili ne bayan gwamnatin jihar ta karɓi kasafin kudin da ya yi matukar yawa daga kwamiti na Musabaƙa na lokacin domin gudanar da taron shekara-shekara na musabakar karatun Alqur’ani.

A shekarar 1995, gwamnatin jihar Kano a karkashin tsohon Gwamnan soja marigayi Abdullahi Wase, ta ware filin mai fadin hekta 2.5 domin gina abin da Cibiyar Musabaƙa wato Musabaqa Village a turance wanda zai kunshi masauki, cibiyar koyon Tahfiz da horaswa, masallaci da kuma wurin cin abinci.

Sai dai, tsawon kusan shekara 23 filin na nan, har zuwa shekarar 2022, lokacin da wani kwamiti da jaridar PT ta ce ta ya nada kansa ya shiga yarjejeniyar haɗin gwiwa da masu zaman kansu PPP da kamfanin Nata’ala.

A watan Agustan 2023, wani shirin sharhi a rediyo mai suna ‘Rigar Kaya’ wanda Yakubu Musa-Fagge ke gabatarwa, ya bankado zargin badakala a wannan yarjejeniya ta PPP.

A cikin shirin, daya daga cikin wadanda ake zargi, Gwani Ɗanzarga, ya ce an gina gidaje 38, inda takwas aka ware wa kwamitin Musabaƙa, sauran 30 kuma aka ba kamfanin Nata’ala.

Amma wasu daga cikin mambobin kwamitin sun ki amincewa da hakan, suka kai ƙorafi ga EFCC. Sai Gwani Ɗanzarga da wasu mutane goma suka garzaya Babbar Kotun Tarayya ta 1 da ke Kano, inda suka shigar da kara na kare haƙƙin ɗan Adam, suna ƙoƙarin dakile binciken EFCC.

Alkalin kotun ya yi watsi da karar, yana mai cewa malamai ba za su iya hana EFCC aiwatar da aikin da kundin tsarin mulki ya dora mata ba.

A ranar Juma’a, alkalin kotun, Musa Shuaibu, ya yanke hukunci a kan karar, inda ya bai wa EFCC damar gayyatar malaman domin gudanar da bincike bisa yadda doka ta tanada.

Haka kuma, alkalin ya ci tarar malaman Naira dubu 250 saboda ɓata lokacin kotu da na EFCC ba tare da sun bayar da hujjar da ke goyon bayan zargin cewa EFCC na gallaza musu ba, alhalin ma sun ki amsa gayyatar hukumar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Dan majalisar wakilan Nijeriya ya sauys sheka daga PDP zuwa ADC

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Tambuwal/Kebbe a jihar Sokoto, Abdussamad Dasuki ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, inda ya koma ADC. A cikin wasiƙar...

Sanata Wamako ya raba wa marayu su 10,000 tallafin N1,000 kowane a jihar Sokoto

Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta Arewa, Aliyu Magatakarda Wamakko, ya bayar da tallafin miliyan 10, ga mutane dubu 10 da...

Mafi Shahara