Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP ya kara kamari, yayin da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya fice daga yarjejeniyar sulhu ta cikin gida da aka cimma a jam’iyyar adawa.
Wike ya zargi gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, kan matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar PDP, yana mai jaddada cewa shi ne ya jawo wannan matsalar.
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, tsohon gwamnan na Rivers ya zargi shugabannin jam’iyyar da suka hada da gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah da cin amana, da rashin gaskiya, da kuma take yarjejeniyar da aka yi da shi.
Ministan ya sha alwashin ci gaba da jan zare har sai ya samu adalci a jam’iyyar.