Hukumomin Saudiyya sun ce ya zuwa yanzu sama da mahajjata miliyan 1.1 ne suka isa kasar domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025.
Babban daraktan kula da takardun shige da fice ne ya bayyana hakan a ranar Talata.
A cewarsa, jimlar maniyyata 1,102,469 ne suka isa kasar Saudiyya daga kasashe daban-daban ta hanyoyin kan tudu da ruwa da Kuma sararin samaniya a karshen ranar Litinin 26 ga watan Mayu.
Daraktan ya kuma bayyana cewa, daga cikin alkaluman, mahajjata 1,044,341 sun isa ta jirgin sama, inda mutum 53,850 ta kan iyakokin kasa, sauran kuma 4,278 ta tashar jiragen ruwa.



