Majalisar dokokin Nijeriya ta ce ta karbi bukatar shugaban kasa Bola Tinubu ta neman sahalewa don cin rancen dala biliyan 21.5 daga waje da kuma bashin Naira Biliyan 758 na cikin gida domin biyan fansho.
Bukatar shugaban wadda aka karanta a zauren majalisar dattawa yayin zaman majalisar na yau, na da nufin samar da kudade don samar da kayayyakin more rayuwa, inganta kiwon lafiya, ilimi, da samar da ruwan sha a kasar.
Majalisar ta mika bukatar ga kwamitin majalisar dattijai mai kula da basussukan cikin gida da waje don ya duba bukatar kuma ana sa ran zai gabatar da rahotonsa nan da makonni biyu.