Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya taya Shugaba Bola Ahmed Tinubu murnar cikar gwamnatinsa shekaru biyu, yana mai cewa shugabanci abu ne mai ɗorewa.
Buhari ya buƙaci a ci gaba da mara wa gwamnatin APC baya, yana mai jaddada cewa gyare-gyare ba sa cimma nasara cikin dare ɗaya.
Cikin takardar taya murna da Mai magana da yawun tsohon shugaban Garba Shehu ya sanya wa hannu, Ya nuna goyon baya ga kokarin rage talauci da hauhawar farashi, yana mai cewa ba gwamnati kaɗai ba ce za ta iya magance matsalolin.
Inda ya ce, Kamfanoni masu zaman kansu da kowane ɗan ƙasa ma su na da rawar da za su taka wajen gyaran Nijeriya.



