Babbar kotun Tarayya da ke Kano ƙarƙashin Mai shari’a Simon Amobeda ta yanke wa Murja Ibrahim Kunya hukuncin watanni shida a gidan gyaran hali ko biyan tarar Naira 50,000, bayan ta amsa laifin cin zarafin Naira.
EFCC ce ta gurfanar da Murja a watan Janairun 2025 bisa karya dokar CBN da ta haramta cin zarafin Naira. An bayar da belinta, amma ta ki bayyana a kotu har sai da aka sake kama ta a ranar 16 ga Maris 2025.
An sake gurfanar da ita a ranar 20 ga Mayu, inda ta amsa laifinta, a hukuncin, kotu ta umurce ta zama jakadiyar EFCC da CBN don wayar da kai kan illar cin zarafin Naira ta hanyar shafinta na sada zumunta.



