DCL Hausa Radio
Kaitsaye

NAHCON ta nemi gwamnatin Saudiyya ta sake ba ‘yan Najeriya damar ci gaba da neman ‘Visa’ don hajjin 2025

-

Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta roki Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya da ta sake buɗe Ƙofar neman biza domin bai wa sauran ‘yan Najeriya damar kammala shirin hajjin 2025.

A wata wasiƙa da ta aike ranar 24 ga Mayu, NAHCON ta bayyana buƙatar a matsayin ta ujila don taimaka wa waɗanda ke cikin rudani samun damar zuwa su sauke farali.

Google search engine

Wannan roƙon ya biyo bayan sanarwar cibiyar Nusuk ta Saudiyya da ta tabbatar da rufe ƙofar bayar da biza, wanda aka fara ware wa har zuwa 29 ga Afrilu, sai aka tsawaita bayan matsin lamba daga shugaban Pakistan.

Ko da yake rufewar ta shafi duk ƙasashen da ke halartar hajji, NAHCON na ƙoƙarin ganin an bai wa Najeriya ƙarin dama, yayin da har yanzu hukumomin Saudiyya ba su ce uffan ba game da lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara