Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta amince da bidiyo uku, ciki har da wanda ke nuna shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, na duba na’urar Radio Biafra da aka ce an shigo da ita ƙasar ta ɓoye.
A ci gaba da shari’ar zargin ta’addanci, Kanu ya ce ya furta wasu kalamai ne cikin tsoro a 2015, sai dai shaida daga DSS ya ce ba a tilasta masa ba, kuma ya karyata zargin barazana daga jami’an DSS.
An kuma shigar da bayanan da Kanu ya rubuta a DSS da bidiyon hirarsa da Sahara Reporters, inda ya kira Najeriya da “Zoo”.
Mai shari’a James Omotosho cikin rahoton da gidan talabijin na Channels ya wallafa ya ce kotun za ta bi diddigin ikrarin da yayi don tantance sahihancin bayanan da DSS ta gabatar.



