Gwamnatin Tarayya ta bayyana niyyarta ta kafa kotun musamman domin hukunta masu laifin magudin jarrabawa, domin zama izina ga wasu.
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana hakan a Abuja yayin karɓar rahoton kwamitin inganta jarrabawa, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Ishaq Oloyede na JAMB.
Ministan kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, ya ce gwamnatin za ta aiwatar da duka shawarwarin kwamitin guda 12, tare da amfani da duk wata hanya wajen yaki da satar amsa a jarrabawa.