Tsohon ministan sufurin kasa a Nijeriya Rotimi Chibuike Amaechi ya ce tun farkon fara maganar takarar Tinubu ya sanar da shi cewa ba zai goyi bayansa ba, kuma ba zai zabe shi ba.
Amaechi ya kara da cewa ya yanke shawarar tsayawa kan kalamansa kuma har yanzu bai taba yi waTinubu aiki ba saboda shugaban ba shi da kwarewar mulkin Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a yayin wani taron taya si murnar cika shekaru 60 da haihuwa da ya gudana a Abuja.
Da yake magana kan hadakar ‘yan adawa, Amaechi ya ce za su goyi bayan ‘yan adawa da za su fitar da ‘yan Nijeriya daga wannan matsala.



