Mamakon ruwan sama na tsawon kwanaki biyu ya haddasa ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa tare da yin sanadin mutuwar mutane akalla 30 a arewa maso gabashin Indiya.
Hukumomin agaji na kasar a wannan Lahadi, sun ce mutane takwas ne suka mutu a yankin Assam, wasu tara a Arunachal Pradesh, mafi yawa daga cikinsu zabtarewar kasa ce ta rutsa da su.
Mahukunta sun fitar da gargadi ga wasu gundumomin da dama a gabascin Indiya, saboda mamakon ruwan sama a cikin kwanaki da suka gabata.
Ruwan saman ya sa kogin Brahmaputra ya cika ya tumbatsa, wanda ya taso daga yankin Himalayas har zuwa kasar Bangladesh.



