Jigo a jam’iyyar APC jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ce hadakar da jam’iyyun adawa ke ci gaba da yi na kalubalantar shugaban kasa Bola Tinubu, ba za ta yi nasara ba.
Mista Oyintiloye, mamba a rusasshiyar majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Lahadi a Osogbo.
Ya shawarci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Peter Obi, da kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wadanda su ne gaba-gaba wajen hadakar, da kada su wahalda kansu da dukiyarsu a kan aikin da ba zai yiyu ba.



