Gwamnatin Jihar Oyo ta raba kayan abinci ga ma’aikatan jihar 2,500, da aka sayar cikin sauki domin saukaka musu yin shagulgulan sallar layya ta shekarar 2025.
Shugaban kamfanin bayar da lamunin noma na jihar, Taofeek Akeugbagold ne ya yi raba kayayyakin a harabar kamfanin da ke a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar Asabar.
Taofeek Akeugbagold yace kayayyakin sun hada da raguna, buhunan shinkafa, man girki, da sauran kayan abinci, kuma fiye da ma’aikata 5000 sun amfana da wannan tsarin zuwa yanzu.
Ya bayyana cewa shirin wani bangare na kokarin Gwamna Seyi Makinde na inganta jin dadin ma’aikatan gwamnatin jihar, musamman a lokucin bukukuwan sallah.



