Wani tsohon dan siyasa kuma mai fada a ji, Cif Adesunbo Onitiri, ya ja kunnen tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsoffin gwamnoni Nasir el-Rufai da Peter Obi kan siyasar 2027.
Cif Onitiri ya gargadi wadannan jiga-jigan ‘yan siyasa musamman a kan yin wanu abu ko kalamai da ka iya dagula siyasar Nijeriya a daidai lokacin da al’ummar kasar ke tunkarar babban zaben 2027.
A wata sanarwa da ya fitar a Legas, Onitiri ya bukaci mutanen uku wadanda ya amince da su a matsayin manyan jigogin siyasar Nijeriya kuma masu fada a ji da su nuna matukar kamun kai da kishin kasa a harkokinsu na siyasa.
Ya nanata cewa karuwar tashe-tashen hankula na siyasa na haifar da babbar barazana ga dorewar dimokradiyyar kasar.



