Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ta ce adadin waɗanda suka mutu sakamakon ambaliya a Mokwa ya kai 153, bayan gano karin gawarwaki biyu a ƙarƙashin gada a ranar Asabar.
Shugaban hukumar, Dr Ibrahim Hussaini, ya ce gawarwakin an binne su ne da safiyar Lahadi. Ambaliyar dai ta afku ne ranar Laraba bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka tafka a daren Talata, inda ta yi sanadin lalacewar dukiyoyi da rushewar wani ɓangare na gadar Mokwa da ke haɗa Arewa da Kudu maso Yamma.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa tuni shugaban ƙasa Bola Tinubu ya tura tawagar gwamnati ƙarƙashin jagorancin Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, don jajanta wa gwamnatin Jihar Neja.



