Kungiyar SERAP mai fafutikar tabbatar da gaskiya da adalci a shugabanci, ta shigar da kara kan kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL bisa gazawarsa wajen bayyana inda kudin da suka kai Naira biliyan 500, da ake zargin bai saka ba a asusun tarayya tsakanin watan Oktoba da zuwa Disamba 2024.
Wannan ya biyo bayan rahoton da Bankin Duniya ya fitar cewa daga cikin Naira tiriliyan 1.1 da kamfanin NNPC ya samu a shekarar 2024, Naira biliyan 600 ne kawai aka sanya a asusun gwamnati, inda aka rasa inda Naira biliyan 500 ta shiga.
Akan haka ne SERAP ta nemi jin karin bayani karkashin dokar ‘yancin bayanai, sai dai kamfanin NNPCL ta hannun lauyansu Afe Babalola, ya ce dokar FOI ba ta aiki kan kamfanin.
Wannan bayanin bai gamsar da kungiyar SERAP ba, hakan ne ya sa ta garzaya babbar kotun tarayya da ke Legas inda ta shigar da kara tana neman kotu ta tilasta wa kamfanin NNPCL ya bayyana inda kudaden suka shiga.



