Gwamnatin Nijeriya ta sanar da ware ranakun Juma’a 6 da Litinin 9 ga watan Yuni, a matsayin ranakun hutu don bukukuwan babbar sallah a kasar.
Ministan cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a cikin wata wasika da babban sakataren ma’aikatar Magdalene Ajani ya fitar.
Ministan ya taya Musulmi murnar sallah da kira gare su kodayaushe su zamo na kwarai don kyautata gobensu.