Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bugun kirjin cewa babu wanda ya isa ya isa ya kore shi daga a PDP ko yace ba dan jam’iyya ba ne.
A martaninsa ga masu kira da a kore shi daga jam’iyyar PDP, cikin wata tattaunawa da manema labarai, Wike ya nanata cewa ya bayar da gagarumar gudumawa wajen gina jam’iyyar, wadda ba kowa ne ya bayar da irinta ba.
Ya bayyana cewa babu wanda ke da hurumi ko kwarin guiwar cire shi daga jam’iyyar da ya yi shekaru da yawa yana hidimtawa, kuma har yanzu dan jam’iyyar PDP ne.
Kalaman na Wike na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun takun saka a cikin jam’iyyar PDP, dangane da yadda yake yi wa gwamnati mai ci aiki da kuma matsayarsa a siyasance.
Nyesom Wike, ya dage kan cewa bai yi wa jam’iyyar PDP zagon kasa ba a zaben 2023, duk da goyon bayan shugaba Bola Tinubu da ya yi.
Ya ce saboda an karya yarjejeniyar da aka kulla ta tsayar da dan takarar shugaban kasa daga kudancin kasar, ta hanyar goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, shine dalilin da ya sa ya janye goyon bayansa.
Wike ya karwa da cewa idan da ya yi zagon kasa, PDP ba za ta ci kujerar gwamna da ‘yan majalisun jihar Rivers ba.