Ministan kasa a ma’aikatar ayyuka Mohammed Goroyo, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na bukatar kashe kimanin naira biliyan 880 a duk shekara domin gyaran titunan kasar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da manajan darakta na hukumar kula da titunan ta tarayya, Chukwuemeka Abbasi ya bayyana cewa, har yanzu hukumar kula da hako danyen mai da sayar da mai ta Nijeriya ba ta fara aiwatar da tsarin cire harajin hanyoyi a kudin man fetur da dizal ba.
Jami’an gwamnatin biyu sun yi wadannan kalaman ne a Abuja, yayin wani zaman bincike da kwamitin majalisar wakilai na wucin gadi ya yi.
Kwamitin na binciken kan yadda ake aiwatar da tsarin biyan kashi biyar bisa dari na masu amfani da hanyoyin mota a karkashin hukumar kula da tituna ta tarayya.