Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da cewa ita da hadin guiwar sauran hukumomin tsaro sun haramta duk wani nau’in hawan daba musamman lokacin bukukuwan sallah babba.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano SP Haruna Abdullahi Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook ta ba al’umma shawarar cewa su kasance masu bin doka da oda a lokuttan shagulgulan sallah.



