Karamin ministan gidaje da raya birane, Yusuf Abdullahi Ata ne ya bayyana hakan a Kano a yammacin ranar Talata, lokacin da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya karbi daruruwan magoya bayan ‘yan jam’iyyar NNPP da suka sauya sheka zuwa APC.
Ya ce a karkashin sabon shirin, za a gina gidaje 77,400 a fadin kasar Nijeriya, inda jihar Kano za ta samu gidaje 4,400 idan aka kammala.