Watanni takwas kenan bayan fashewar dam din Alau wanda ya haddasa barna tare da janyo asarar rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa a Jihar Borno, har yanzu ba a fara aikin gyaran da gwamnati ta yi alkawari ba.
Jaridar Daily Trust ta yi wani dogon nazari a karshen mako kan wannan batun, inda ta rawaito cewa al’ummar Alau, Maiduguri da sauran kauyuka a Jihar Borno na ci gaba da rayuwa cikin fargaba sakamakon abin da suka kira gazawar gwamnatin tarayya na gyara bangaren dam din da ya rushe da hakan ya jaza ambaliya mai muni a bara.
A kwanakin baya, yankunan Alau da na Maiduguri sun fara samun ruwan sama na farko a shekarar 2025, kuma ana sa ran za a yi mamakon ruwan sama a cikin kwanaki masu zuwa.
Mazauna yankin sun bayyana bukatarsu da a gaggauta gyara dam ɗin domin kauce wa maimaita ambaliyar ruwa da ta faru a ranar 10 ga Satumba, 2024, wadda ta mamaye Maiduguri, ta hallaka mutane fiye da ɗari, tare da raba sama da mutum miliyan ɗaya da muhallansu.
Bayan aukuwar wannan iftila’i, jami’an gwamnati sun dora laifin kan sauyin yanayi, amma masana da mazauna yankin sun riga da sun alamta cewa dam ɗin na fuskantar barazanar rushewa, amma ba a ɗauki wani mataki ba kafin abun ya faru.
A ranar 5 ga Fabrairu, 2025, Majalisar Zartaswa ta Ƙasa (FEC) ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta amince da kashe naira biliyan 80 domin sake ginawa da gyaran dam ɗin don hana faruwar irin wannan bala’i a gaba.
A ranar 1 ga Maris, Ministan Ruwa da Tsabtace Muhalli, Injiniya Joseph Utsev, ya kaddamar da aikin, wanda ya bayyana cewa za a kammala cikin watanni 24.
Utsev ya ce aikin zai kasance a matakai biyu: na farko zai gudana daga Maris zuwa Satumba 2025, kuma zai mayar da hankali kan dakile hatsarin ambaliya a jihar. Na biyu kuma, wanda zai fara daga Oktoba har zuwa kammala aikin, zai shafi fitar da laka da ƙarfafa tsarin ginin dam ɗin don tabbatar da dorewarsa.
Sai dai, bayan shafe wata biyu daga ranar da aka ƙaddamar da aikin mataki na farko, jaridar Daily Trust ta kai ziyara Alau don duba matsayin aikin, amma babu wani abin da ke nuna cewa an fara shi. Sannan, Babu kayan aikin da suka isa da za a nuna ana shirin fara aikin nan ba da jimawa ba, duk da hasashen minista cewa ana iya fuskantar wata ambaliya a jihar.
Bisa hasashen Hukumar Hasashen Yanayi ta Ƙasa (NIMET), Jihar Borno na daga cikin jihohi 30 da ake sa ran za su fuskanci ambaliya daga watan Mayu zuwa Nuwamba, 2025. Da wasu ke ganin Abin takaici ne, a ce aikin bai fara ba har yanzu.
Tambayar da yawancin mazauna Alau da Maiduguri ke ta yi ita ce: “Shin hukumomin Najeriya sun ɗauki darasi? Ko kuma tarihi zai maimaita kansa?”
A wata hira jaridar ta yi da, yawancin mazauna Alau sun nuna rashin jin daɗinsu ga gwamnatin tarayya saboda gazawarta wajen tura kayan aiki domin fara aikin.
Wata matar aure a Alau, Hajara Lawan, ta ce duk ƙauyen na cikin fargabar abin da ka iya faruwa idan ba a gyara dam ɗin ba.
Kazalika, jaridar ta kuma lura cewa na’urori biyu kacal ne (cranes) aka gani ajiye a sama kusa da dam ɗin Alau.
Mai garin Alau, Bulama Kadai, ya gargadi gwamnati kan hatsarin da ke tafe idan aka ci gaba da jinkirta aikin. Ya ƙara da cewa sai da ya yi amfani da hikima sosai kafin ya shawo kan wasu matasa da suka shirya yin zanga-zanga a makon da ya gabata.
A ranar 24 ga Disamba, 2024, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi kira ga gwamnatin tarayya cewa damina na ƙaratowa, don haka akwai gaggawar bukatar sake gina dam ɗin da ya rushe.
Da aka tuntubi Engr Abdullahi Abubakar, jami’in kula da inganci a Ma’aikatar Ruwa ta Tarayya reshen Jihar Borno, ya ce ba shi da hurumin magana kan batun.
Haka kuma, jaridar ta kai ziyara Hedikwatar Hukumar Raya tafkin Chadi (LCBDA), inda mai magana da yawun hukumar, Muhammad Bukar, ya ce ba shi da hurumin yin magana kan kwangilar dam ɗin.



