DCL Hausa Radio
Kaitsaye

PDP ta roki Shugaba Tinubu da ya sake bita kan farashin litar fetur da na lantarki a Nijeriya

-

Jam’iyyar PDP a Nijeriya ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya sake duba dukkanin tsare-tsaren da suka zama alakakai ga jama’ar kasar.

Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar PDP, Mr Debo Ologunagba ne ya gabatar da wannan kokon barar a cikin sakon barka da sallah da ya aike wa ‘ya’yan jam’iyyar.

Google search engine

Jam’iyyar ta roki gwamnati da ta rage farashin man fetur, kudin wutar lantarki da wasu kudaden da ake cajin mutane.

Haka kuma sanarwar ta kara jan hankalin Shugaba Tinubu da ya yi amfani da shekaru 2 da suka rage masa wajen inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su kasance ‘yan kasa na gari da kuma dagewa da addu’a da kuma yin tawakkali duk da matsin tattalin arzikin da ake fama da shi da kuma matsalolin tsaro da ya addabi kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Hukumar Tarayyar Turai ta yi Allah-wadai da haramta biza da Amurka ta yi wa wasu Turawa

Tarayyar Turai, tare da ƙasashen Faransa da Jamus, sun yi kakkausar suka ga matakin Amurka na haramta biza ga wasu ’yan Turai da ke yaki...

Shugaba Tinubu ya yi kira ga hadin kai da hakuri a tsakanin addinai a cikin sakon taya murnar bikin Kirsimeti

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su rungumi haɗin kai, juriya da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai, yana mai cewa...

Mafi Shahara