A ranar Talata ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu tare da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, suka kaddamar da ginin da aka gyara wanda aka sanyawa sunan shugaban kasa.
Sai dai ana ci gaba da nuna damuwa kan kudin da aka kashe gyaran ginin, wanda ya lakume zunzurutun kudi har Naira biliyan 39, adadin ya ninninka Naira miliyan 240 da gwamnatin tsohon Shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida ta gina dakin taron a shekarar 1991, sau 162.
Wannan na zuwa ne yayin da ake fama da tabarbarewar a fannin kiwon lafiya da ilimi a Nijeriya.