Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Tadurga a karamar hukumar Zuru ta jihar Kebbi a daren Litinin, inda suka kashe mutane, suka yi garkuwa da wasu, tare da sace dabbobi da kayayyaki.
Wani mazaunin kauyen, Audu Sule, ya ce maharan sun rika harbi ba kakkautawa, yayin da wani, Abdullah Zuru, ya ce harin ya faru ne bayan wani dan lokaci na zaman lafiya da ya bai wa manoma damar girbi.
Gidan talabijin na Channels ya ce, har zuwa hada rahoton hukumomi ba su fitar da cikakken bayani kan adadin mutanen da aka kashe ko aka sace ba.