Tinubu ya sauka ne a sansanin sojin saman Nijeriya dake Makurdi, da misalin karfe 12:58 na rana.
Rahoton gidan talabijin na Channels yace ana sa ran shugaban zai gana da manyan masu ruwa da tsaki a jihar duba da munanan hare-haren da suka haddasa ajalin mutane a jihar.
Gabanin zuwan Shugaba Tinubu gwamnatin jihar ta bayar da hutu ga ma’aikata a ranar Laraba yayin da shugaban ke ziyarar aiki da kokarin tabbatar da zaman lafiya a jihar.