DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shirin kafa jam’iyyar ADA shiririta ce, kawai domin yaudarar jama’a da sunan siyasa – Festus Keyamo

-

Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ya bayyana cewa sabuwar jam’iyyar siyasa ta ADA ba zata iya zama barazana ga jam’iyya mai mulki, APC, ba.

Keyamo ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce kafa jam’iyyar ADA ba ta yi kama da irin haɗin gwiwar da aka yi wajen gina APC a shekarar 2013 ba.

Google search engine

Jam’iyyar ADA na samun goyon bayan wasu fitattun ‘yan siyasa, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Jaridar Dailytrust ta ruwaito cewa tuni aka mika takardar neman rajistar jam’iyyar ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a ranar 19 ga Yuni, 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

INEC na duba buƙatun kungiyoyi 110 da ke neman rigista a matsayin jam’iyyun siyasa a Najeriya

Hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana cewa ta karɓi wasikun buƙatun rajistar sabbin jam’iyyu 110 daga kungiyoyi daban-daban har zuwa Litinin, 23 ga watan...

PDP ta maido wa Samuel Anyanwu mukaminsa na sakataren jam’iyyar na kasa

PDP ta maido wa Samuel Anyanwu mukaminsa na sakataren jam'iyyar na kasa Jam’iyyar PDP ta dawo da Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyya na kasa bayan...

Mafi Shahara