Gidajen man fetur mallakin NNPCL sun yi gyare-gyare kan farashin man fetur, zuwa Naira 945 akan kowace lita a babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin.
Haka kuma farashin ya ƙaru zuwa Naira 915 kowace lita a wasu gidajen man ta da ke Legas.
Karin ya nuna cewa an samu Naira 45 da Naira 35 ya karu a farashin baya a biranen Legas da Abuja.
Gyaran farashin dai ya zo ne kwanaki kadan bayan da matatar mai ta Dangote ta kara farashin man fetur daga Naira 825 zuwa Naira 880 kan kowace lita.
Jaridar Punch ta rawaito cewa an fara amfani da sabon farashin a gidajen mai da dama mallakin kamfanin na NNPCL.