Leone Julius Maada Bio, Shugaban kasar Sierra, wanda shi ne zababben shugaban kungiyar ta ECOWAS, ya yi alkawarin mayar da hankali wajen maido da tsarin mulki da zurfafa dimokaradiyya a yankin kasashen yammacin Afirka.
Ya karbi ragamar shugabancin ECOWAS daga hannun shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya a ranar Lahadi a Abuja, a taron hukumar karo na 67, da ya gudana.
Tinubu ya yi wa’adi biyu ne a matsayin shugaban kungiyar ta ECOWAS.
A jawabinsa bayan karbar ragamar, shugaba Bio ya yi alkawarin jagorantar sabuwar kungiyar ECOWAS mai kishin jama’a da kuma aiwatar da ayyukan ci gaba a daidai lokacin da ake fuskantar kalubale da damammakin da ba a taba gani ba a yankin yammacin Afirka.