Matatar mai ta Port Harcourt da ke karkashin kamfanin man Nijeriya NNPCL ta kwashe fiye da wata guda a rufe saboda gyara, ba ta dawo aiki ba.
Wannan na zuwa ne bayan da Tsohon jami’in hulda da jama’a na NNPC, Olufemi Soneye, ya bayyana a watan Mayu cewa za a rufe matatar don gyare-gyare.
Rahotanni sun ce hukumar EFCC na binciken kudaden da aka ware don gyaran matatun mai uku a Nijeriya da suka hada da: dala biliyan $1.5 don matatar mai ta Port Harcourt, da dala miliyan $740m don matatar man Kaduna, da kuma dalar Amurka miliyan $657m don Warri.
Yanzu haka dai tsoffin shugabannin matatun, ciki har da Umar Isa (Tsohon CFO na NNPC), suna fuskantar bincike kan zargin almundahana da karkatar da kudi kamar yadda jaridar Punch ta gano.



