DCL Hausa Radio
Kaitsaye

INEC na duba buƙatun kungiyoyi 110 da ke neman rigista a matsayin jam’iyyun siyasa a Najeriya

-

Hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana cewa ta karɓi wasikun buƙatun rajistar sabbin jam’iyyu 110 daga kungiyoyi daban-daban har zuwa Litinin, 23 ga watan Yunin, 2025.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce ana ci gaba da duba buƙatun bisa doka da tsarin da aka shimfiɗa inda ya ce sun riga sun amsa duk buƙatun da aka aika, banda guda shida da za a amsa kafin ƙarshen mako.

Google search engine

Hukumar ta INEC ta fitar da cikakken bayanan jerin sunayen kungiyoyin da ke neman rajista da sunayensu, takaitattun haruffansu, adireshisu, da shugabanninsu a jumlace.

Kuma hukumar cikin sakon da ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce za a wallafa jerin gwanon su a shafin yanar gizo da kafafen sada zumunta na hukumar don samun gamsashshiyar fahimta kan kudirin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

PDP ta maido wa Samuel Anyanwu mukaminsa na sakataren jam’iyyar na kasa

PDP ta maido wa Samuel Anyanwu mukaminsa na sakataren jam'iyyar na kasa Jam’iyyar PDP ta dawo da Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyya na kasa bayan...

Tsohon Gwamnan jihar Kwara Cornelius Adebayo ya rasu

Tsohon Gwamnan jihar Kwara kuma Ministan Sadarwa na baya, Cornelius Adebayo, ya rasu yana da shekara 84 a Abuja da safiyar Laraba nan. Babban dansa Oluwasegun,...

Mafi Shahara