Tsohon Gwamnan jihar Kwara kuma Ministan Sadarwa na baya, Cornelius Adebayo, ya rasu yana da shekara 84 a Abuja da safiyar Laraba nan.
Babban dansa Oluwasegun, ne ya tabbatar da rasuwar cikin wata sanarwa da jaridar Premium Times ta samu, yana mai cewa Adebayo ya rasu ne da safiyar 25 ga Yuni, 2025.
Marigayin ya taba zama kwamishinan ilimi a Jihar Kwara tsakanin 1975 zuwa 1978, kuma an zabe shi Sanata a shekarar 1979 karkashin jam’iyyar adawa ta Unity Party of Nigeria a lokacin da Najeriya ta koma mulkin farar hula a Jamhuriyya ta Biyu.
Daga nan kuma tsohon shugaban kasa Obasanjo ya nada shi mukamin ministan Sadarwa da harkokin sufuri tsakanin shekarar 2003 zuwa 2007.