DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Cristiano Ronaldo ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyarsa ta Al Nassr har zuwa shekarar 2027

-

Cristiano Ronaldo ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyar Al Nassr ta kasar Saudiyya a hukumance, inda zai ci gaba da zama a birnin Riyardh na kasar har zuwa shekarar 2027.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, inda a hoton Ronaldo yake rike da riga mai lamba “2027” tare da shugaban kungiyar Al Nassr, Abdullah Almajid.

Google search engine

Sanarwar ta tabbatar da cewa Ronaldo, wanda kuma ke rike da mukamin kyaftin din kungiyar, zai ci gaba da aiki tare da Al Nassr na tsawon shekaru biyu.

Ronaldo ya kuma bayyana jin dadinsa a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan sandan jihar Katsina sun musanta labarin barayin daji sun karbe ikon karamar hukumar Kankara ta jihar

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta ce tana sane da wani labari da ta kira na karya da ake yadawa musamman a kafar sadarwar X...

Mataimakin shugaban Nijeriya Kasshim Shettima ya tafi kasar Ethiopia

A safiyar ranar Alhamis Kasshim Shettima ya tashi daga Abuja zuwa birnin Adis Ababa domin ziyarar aiki bisa gayyatar da Firaministan kasar Dr Abiy Ahmed...

Mafi Shahara