DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Mun nemi INEC ta yi wa Tafiyar Matasa rijista a matsayin jam’iyyar siyasa da sunan “Access Party” – Bulama Bukarti

-

Jagoran Tafiyar Matasa, Barista Audu Bulama Bukarti, ya bayyana cewa sun mika bukatar yi wa tafiyar matasa rajista a matsayin jam’iyyar siyasa da sunan “Access Party”.

Barr Bulama Bukarti ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce sun nemi rejista da sunan Access Party ne saboda sauĆ™in shi da kuma ma’anarsa na bawa nagartattun matasa sabbin jini dama su kawo sabbin manufofi a tsarin siyasa da mulkin Nijeriya.

Google search engine

 

Bulama ya ce manufarsu ita ce bai wa waÉ—anda suka dace da jagoranci al’umma damar shigowa su kawo gyara a Ć™asarsu,saboda haka Access Party ita ce jam’iyar Tafiyar Matasa, kuma kirarinta a Arewa zai ci gaba da zama haka, a kudancin Nijeriya kuma a kirata “Na Our Waka. Na Our Mata”.

Ya kara da cewa akwai karin bayani game da halinda suke ciki da hukumar zabe ta kasa INEC amma zuwa nan gaba za su bayyana halin da ake ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Cristiano Ronaldo ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyarsa ta Al Nassr har zuwa shekarar 2027

Cristiano Ronaldo ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyar Al Nassr ta kasar Saudiyya a hukumance, inda zai ci gaba da zama a birnin Riyardh na kasar...

Mataimakin shugaban Nijeriya Kasshim Shettima ya tafi kasar Ethiopia

A safiyar ranar Alhamis Kasshim Shettima ya tashi daga Abuja zuwa birnin Adis Ababa domin ziyarar aiki bisa gayyatar da Firaministan kasar Dr Abiy Ahmed...

Mafi Shahara