Indomie, shahararren kamfanin taliyar Indomie a Najeriya, ya ƙaddamar da sabon gangami mai taken “Ingantaccen Abinci Domin Nasara”. Wannan gangami yana jaddada muhimmancin abinci mai gina jiki kamar Indomie wajen tallafa wa nasarar iyalai da ƙara lafiyarsu, musamman a Arewacin Najeriya.
Shekaru da dama kenan da aka san Taliyar Indomie da inganci, daɗi da sauƙin samu a gidajen ‘yan Najeriya. Sabuwar tallar talabijin ta Ingantaccen Abinci Don Nasara ta mayar da hankali ne kan wannan manufa, inda ta ke bayyana Indomie a matsayin abokiyar tafiya ta nasarar iyalai a faɗin ƙasar.
*Nasara Ta Hanyar Abinci Mai Gina Jiki*
An ƙaddamar da wannan gangami ne a ranar 6 ga watan Yuni, 2025. “Muna so mu ƙara jaddada yadda Indomie ke jajircewa wajen tallafa wa iyaye mata da iyalai ta hanyar samar da abinci mai daɗi, mai sauƙin samu kuma cike da sinadaran gina jiki, wato abinci da ke ƙara kuzari da cimma burin rayuwa,” in ji wakilin kamfanin.
Cikin tallar talabijin ɗin, an ba da labarin Binta, wata yarinya a Najeriya da ke da burin zama likita. Soyayya da abinci mai gina jiki da mahaifiyarta ke ba ta ne ya zame mata tsanin burinta. Tallar ta bi rayuwar Binta daga ƙuruciya zuwa lokacin da ta shiga makarantar koyon aikin likita, abin da ya nuna yadda abinci mai kyau da goyon bayan iyali ke ba da gudunmuwa wajen cimma nasara. A duk tafiyar rayuwarta, Indomie na tare da ita a matsayin abincin da ya kasance da ita tun farko. Za a iya kallon faifan tallar a Manhajar YouTube
labarin rayuwar Binta da ya ke jaddada muhimmanci abinci mai gina jiki da goyon bayan iyali.
*Taliya Mai Cike da Sinadaran Gina Jiki*
Indomie na ɗauke da sinadaran da ke da matuƙar amfani ga jiki kamar calcium, iron, protein, Vitamin B da Vitamin A. Waɗannan sinadarai na taimakawa wajen haɓaka jiki, bunƙasa kwakwalwa da kuma ƙarfafa lafiya mai ɗorewa. Hakan ya sa Indomie ta zama ɗaya daga cikin abincin da kowa ke iya dafa wa cikin sauƙi, tare da ɗanɗano mai daɗi da sinadarai masu amfani.
“Muna alfahari da ƙaddamar da gangamin Nasara Da Indomie, wanda ke nuna gudunmuwar da abinci mai gina jiki ke badawa wajen gina rayuwa mai kyau,” in ji Jamiu Abdulrasheed, jami’in kula da tallace-tallace na sashen zamani na Indomie.
“Wannan girmamawa ce ga iyaye mata masu sadaukarwa wajen ciyar da ‘ya‘yansu da abinci mai amfani, da kuma yadda Indomie ke haɗa daɗin ɗanɗano da gina jiki don tallafa musu wajen cimma nasara.”
An ƙarfafa masu kallo su duba wannan labari mai cike da ƙarfafawa na Ingantaccen Abinci Don Nasara a shafukan sada zumunta:
@IndomieArewa a Facebook da @indomie_arewa a Instagram.
Indomie Nigeria na ci gaba da jajircewa wajen samar da hanyoyin abinci masu gina jiki ga iyalai da tallafa musu wajen cimma nasara.