DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Rundunar sojin saman Nijeriya sun yi ajalin ‘yan bindiga da dama a jihar Neja

-

Sojojin saman Nijeriya dake karkashin rundunar Operation Fansar yamma, sun yi luguden wuta ga ‘yan bindiga da suka kai hare-hare na baya-bayan nan a jihar Neja, tare da tallafi ta kasa daga sojojin kasar.

Harin wanda aka aiwatar tsakanin 24 zuwa 26 ga watan Yuni, 2025, an gudanar da su ne bisa ingantattun bayanan sirri, a cewar sanarwar da daraktan yada labarai na rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar ranar Juma’a a Abuja.

Google search engine

Ya ce rundunar, hadin gwiwa sauran hukumomin tsaro, sun gano ‘yan ta’adda masu kai hare-hare da satar shanu a yankunan Kakihun da Kumbashi.

Cikin hanzari rundunar ta tura da jirage domin kai hare-hare wanda aka yi nasara tare da lalata musu kayayyaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara