Bayanai sun fara fita dalla-dalla kan dalilan da suka sa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya yi murabus daga mukaminsa a ranar Juma’a.
Rahoton da jaridar PUNCH ta samu daga majiya mai ƙarfi ya nuna cewa Ganduje ya ajiye mukaminsa ne saboda rahotannin cewa tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, na shirin shiga jam’iyyar APC.
Tun da misalin ƙarfe 3 na rana a ranar Juma’a, wasu da ke aiki a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa sun shaida wa jaridar cewa tsohon shugaban jam’iyyar ya fara barazanar yin murabus saboda yarjejeniyar da aka ce ta faru tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Kwankwaso don shigar Kwankwaso jam’iyyar.
Wata majiya ta bayyana cewa duk manyan jami’an jam’iyyar, ciki ha da sakataren jam’iyya na ƙasa, Ajibola Basiru, sun yi ƙoƙarin hana Ganduje ajiye mukaminsa.
Gaskiya banji dadin ajiye aiki shi ba, domin wlh ganduje yafi kwankwaso nesa ba kusan ba