Wasu daga cikin al’ummar jihar Borno sun zargi murabus din Ganduje a matsayin wata maƙarƙashiya da aka shirya domin a kawar da Kassim Shettima a gwamnatin Tinubu a zaben shekarar 2027, kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.
A yammacin ranar Juma’a ne dai Ganduje ya yi murabus daga mukaminsa na shugabancin jam’iyyar APC, inda nan take aka rantsar da mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa daga yankin (Arewa), Ali Dalori a matsayin shugaban riko.
Dalori dai ɗan asalin jihar Borno ne wadda ita ce jihar da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya fito.
Kodayake Ganduje ya ce ya yi murabus ne bisa dalilai na kula da lafiyarsa,
Sai dai jita-jita na nuna cewa ‘yan jam’iyyar ne suka tilasta masa yin murabus don ba da damar sake fasalin tsarin shugabancin jam’iyyar kafin babban zaben Nijeriya na shekarar 2027.