Hukumar kula da aikin hajji NAHCON ta ce ta kammala aikin dawo da alhazai gida daga kasar Saudiyya bayan kammala aikin Hajjin bana, 2025.
Jirgin karshen ya tashi daga birnin Jeddah da misalin karfe 10:30 na safiyar Talata, inda ya sauka a Kaduna dauke da mahajjata 87.
Aikin dawo da mahajjatan ya dauki kwanaki 17 tun bayan fara shi a ranar 13 ga watan Yuni, kuma ya gudana cikin nasara ba tare da wata matsala ba, kamar yadda wata sanarwa daga Fatima Sanda Usara jami’a a sashen yada labaran hukumar ta sanar.