DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Mutanen da siyasa ta yi wa ritaya ne ba sa ganin ayyukan Tinubu – Nyesom Wike

-

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa duk wanda bai ganin nasarorin da shugaba Bola Tinubu ke samu ba, to lallai siyasar sa ta kai karshe.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito Wike na bayyana hakan a yayin kaddamar da ayyukan tituna daga Ushafa zuwa Bwari a Abuja, inda ya ce masu sukar tafiyar gwamnatin Tinubu suna kokarin raina ci gaban da ake samu.

Google search engine

Ya kara da cewa yawancin masu suka sun dade suna yawon jam’iyya tun daga 1999 ba tare da wani abin a zo a gani da suka samar ba, amma yanzu suna neman hana Tinubu damar yin aiki.

Ministan ya ce gwamnatin Tinubu tana aiwatar da ayyuka a sassa daban-daban na kasar, kuma duk wanda ya gaza gane hakan, ko dai makaho ne ko kuma son zuciya ne ya rufe masa ido.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara