Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, ya bayyana dalilin da ya sa ya shiga hadakar jam’iyyu na adawa da ke kokarin kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2027.
Gidan Talabijin na Channels ya Ambato Peter Obi a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, Obi ya ce babu wata kungiya guda da za ta iya sauya Najeriya ita kadai.
Ya jaddada cewa dole ne hada karfi wuri daya don rushe tsarin da ke hana ci gaban al’umma.
Obi ya kara da cewa sun kuduri aniyar hadin gwiwa don samar da shugabanci nagari, mai jin kai da kwarewa wanda zai baiwa jin dadin ‘yan kasa fifiko.
Taron hadin gwiwar na adawa ya gudana ne a cibiyar Yar’Adua da ke Abuja, inda aka sanar da jam’iyyar ADC a hukumance a matsayin dandali na zaben 2027.



