Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa sabuwar Cibiyar taro ta Ƙasa da Ƙasa mai suna Bola Ahmed Tinubu da aka kaddamar kwanan nan, ta samar da naira miliyan 650 a cikin mako uku kacal.
Wike ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, 3 ga Yuli.
Jaridar The Nation ta ruwaito ministan na cewa kafin gyaran cibiyar, ana samun naira miliyan 50 ne kawai a shekara daga dakin taron.
Wike ya ƙara da cewa a baya-bayan nan shugaban kasa ya karɓi shugabannin ECOWAS a wajen, kuma jakadun kasashe sun yaba matuƙa da ingancin gyaran da aka yi wa cibiyar.