Jam’iyyar Labour karkashin jagorancin Julius Abure ta bai wa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, wa’adin sa’o’i 48 da ya fice daga jam’iyyar, bisa dalilin shiga hadakar jam’iyyun adawa da ke shirin kalubalantar APC a 2027.
A wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na kasa, Obiora Ifoh, ya fitar a Abuja, ya ce ba su da hannu a cikin wannan hadaka, yana mai zargin cewa yawancin wadanda ke ciki suna fi ba da fifiko ga kare muradun kansu ba na jama’a ba.
Obiora ya ce jam’iyyar ba za ta lamunci kasancewa da ’yan siyasa masu fuska biyu ba, inda ya bukaci duk wani mamba da ya shiga hadakar jam’iyyun adawa da ya fice cikin sa’o’i 48 kamar yadda rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.