Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya zargi masu adawa da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da yin amfani da wahalar da ’yan Najeriya ke fuskanta a matsayin makami na siyasa, yana mai cewa jam’iyyar adawa ta PDP ce kaɗai ke da ikon kalubalantar Tinubu a 2027, muddin ta magance rikicin da take ciki.
Wike ya bayyana hakan ne yayin taron sa da ’yan jarida na wata-wata da yake gudanarwa a Abuja a ranar Alhamis.
Ya caccaki shugabannin da suka taba riƙe madafun iko a baya, yana cewa yawancinsu sun yi shiru ko kuma sun kasa saukaka rayuwar talakawa lokacin da suke kan mulki.