Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Lakurawa ne sun kai mummunan hari a kauyen Kwalajiya da ke ƙaramar hukumar Tangaza a jihar Sakkwato, inda suka yi ajalin mutane 15, tare da jikkata wasu da dama.
Harin, wanda ya faru da misalin karfe 2:00 na rana a ranar Talata, na da alaka da ramuwar gayya bayan kawar da wasu mambobin kungiyar uku, ciki har da wani shugaban su da ake zargi, a wani yunkurin harin da bai yi nasara ba da suka kai a baya.
Jaridar Daily Trust ta ambato rundunar ƴan sandan jihar Sakkwato ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin mai magana da yawunta, DSP Ahmed Rufa’i, inda ya ce ana ci gaba da tantance adadin wadanda harin ya rutsa da su.
Wannan hari na daga cikin jerin hare-hare da kungiyar Lakurawa ke ci gaba da kaiwa yankunan karkara a Tangaza, inda suka dauki rayukan mutane a Sabiyo da Baiji da Hurumi cikin makonni da suka wuce.