Hedikwatar tsaro ta ƙasa ta bayyana cewa dakarun sojin Najeriya sun yi ajalin fitattun ‘yan ta’adda da dama tare da cafke wasu 1,191 a fadin manyan ayyukan tsaro daga watan Afrilu zuwa Yuni 2025.
Daraktan hulɗa da jama’a na harkokin tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja, inda ya gabatar da rahoton ayyukan sojin a zangon biyu na shekarar 2025.
Ya ce dakarun Operation Hadin Kai, Fasan Yamma, Safe Haven, UDO KA da Operation Delta Safe, sun nuna bajinta matuƙa wajen dakile ayyukan ta’addanci a wannan lokaci.
A cewarsa, daga cikin manyan ‘yan barayin daji da aka kawar akwai Amir Abu Fatimah, Kinging Auta, Abdul Jamilu, Salisu, Malam Jidda, Maiwada, Mai Dada da kuma Nwachi Eze wanda aka fi sani da Onowu kamar yadda Premium Times ta ruwaito.