Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, mai shekara 82, na karɓar magani a birnin Landan tun daga watan Afrilu.
Buhari, wanda ya sauka daga mulki a 2023 bayan kammala wa’adin mulki na biyu, ya fara tafiya ne don duba lafiyarsa, amma daga bisani ya kamu da rashin lafiya tare da shafe kwanaki a dakin kulawa ta musamman (ICU).
DW Africa ta ruwaito mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya tabbatar da cewa Buhari na fama da rashin lafiya kuma yana jinya a Landan, amma bai bayyana asalin cutar ko asibitin da yake kwance ba.
Ana sa ran zai dawo gida Najeriya da zarar ya murmure.