Ana cigaba da samun rahotannin sauyin sheka a majalisar wakilai, yayin da ’yan majalisa bakwai daga Jihar Akwa Ibom suka koma jam’iyyar APC. Wadanda suka sauya shekar sun hada da mutane shida daga PDP da daya daga YPP.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito kakakin majalisar cewa Tajudeen Abbas, ne ya karanta wasikun sauya shekar a zaman majalisar na ranar Alhamis, inda suka ce rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP a matakin jiha da na kasa ne ya sa suka fice.
Sai dai shugaban marasa rinjaye na majalisar, Hon. Kingsley Chinda, ya bayyana bakin ciki da matakin, yana mai cewa zargin rikici a PDP ba shi da tushe, kuma bai dace da doka ba.
Abun da ya sanya ya bukaci kakakin majalisar da ya yi aiki da sashi na 68 (1) (g) na kundin tsarin mulki, ta hanyar ayyana kujerunsu a matsayin za’a sake zaben su.